Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar gudanarwar kasar Sin ta samar da yuan biliyan 100 don sake raya kasa bayan bala'in ambaliyar ruwa
2020-08-27 10:52:50        cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira taro a jiya Laraba, inda ta shirya gudanar da wasu ayyukan yaki da ambaliyar ruwa da ceto da sake farfado da yankuna bayan bala'in.

Taron ya bayyana cewa, yawan kudin da kwamitin tsakiyar kasar da kanakan hukumomi za su yi amfani da shi wajen sake farfado da yankuna bayan bala'in, ya kai kimanin yuan biliyan 100, kuma an tsara samar da kudi kai tsaye zuwa yankuna masu fama da bala'in.

Kwamitin tsakiya zai kara samar da tallafin kudi ga wadanda gidajensu suka lalace a yankunan da suka fi fama da talauci, da kuma taimakawa wajen gyara gine-gine da kayayyakin aikin gona na zamani da suka lalace sakamakon bala'in, da samar da irin shuka da sauransu. Baya ga haka, za a gaggauta gyara hanyoyin mota, da gadoji, da aikin adana ruwa da dai makamantansu. Kana taron ya tabbatar da fannonin da za a dora muhimmanci a yayin da ake kokarin sake farfado da yankuna bayan bala'in. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China