Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe da yankuna 42 sun ba da tabbacin halartar bikin baje kolin CIFIT da za a shirya a kasar Sin
2020-08-27 11:09:43        cri
Rahotanni na nuna cewa, yanzu haka kasashe da yankuna 42, sun tabbatar da aniyarsu ta halartar bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasar Sin na kasa da kasa (CIFIT) da babban taron zuba jari kan shawarar ziri daya da hanya daya, da za a gudanar a cikin wannan shekara a kasar Sin.

Bikin da zai gudana daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Satumba a birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin, zai mayar da hankali ne kan taken da suka hada da sabbin ababen more rayuwa, da cinikayyar yanar gizo, da kimiya da fasahar kirkire-kirkire.

A wannan shekara, bikin na CIFIT ya kuma hada gwiwa da rukunin kamfanin Alibaba, wajen kafa dandalin yanar gizo, da zai rika samar da hidimomin taruka ta kafar bidiyo ga manyan kasashe da yankuna da za su halarci bikin.

Manufar bikin baje kolin da majalisar gudanawar kasar ta amince da shi, ake kuma shirya shi a watan Satumban kowace shekara a birnin Xiamen, ita ce bunkasa alaka da musaya tsakanin manyan kafofin tattalin arziki da cinikayya da yin hadin gwiwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China