Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Shenzhen dake samun ci gaba cikin sauri
2020-08-27 14:48:14        cri

A yayin taron murnar cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara aiwatar manufar yin gyare-gyare, da bude kofa ga ketare, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, samarwa al'ummun Sinawa yanayin rayuwa mai kyau, tare kuma da farfado da al'ummun kasar Sin, babban aiki ne na 'yan JKS, kana shi ne burin gwamnatin kasar, yayin da take aiwatar manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare.

A matsayinsa na wani sabon birni dake samun ci gaba cikin sauri a kasar Sin, birnin Shenzhen, ya kasance yankin musamman na tattalin arziki na farko na kasar, lamarin da ya jawo hankalin masu zuba jari na kasashe daban daban.

Ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana¡K

Wasu alkaluma da aka fitar sun nuna cewa, mutum daya cikin 4 na mazauna birnin ya taba kafa wani kamfani na kansa. Zhang Zhaohui, wanda ya kammala digiri na uku a wata jami'a a birnin Xi'an, yana daya daga cikinsu. Ya ce, a lokacin da ya gama katarunsa a jami'a, yana da zabi guda biyu, daya shi ne aiki a birnin Xi'an, wato, wurin da yake zama, dayan kuma shi ne, zuwa birnin Shenzhen. Ya ce, "Ba ni da abokai a wannan birni, amma na tsaida wannan kuduri na musamman, wato kafa kamfani a birnin Shenzhen, domin ina son sarrafa na'urorin kwamfuta a wani wurin da ya fi samun bunkasuwa a wannan fanni."

Bugu da kari, sabon birnin yana janyo hankalin matasan da suka shigo birnin domin cimma burinsu, duba da cewa gwammatin birnin, tana yin iya kokarin ta na ba su goyon baya. Alal misali, gwamnatin birnin ta kafa hadadden dandalin samar da hidima ga matasa, wadanda suka zo Shenzhen don kafa kamfanoni, dandalin da ya kasance irinsa na farko a kasar Sin.

Baya ga kasancewar dandalin na samar da wurin kwana har tsawon kwanaki bakwai ga matasan da suka isa birnin a karo na farko, a daya hannun kuma, yana ba su shawarwari yayin da suke neman aikin yi, inda kawo yanzu, irin wadannan dandalolin da aka kafa a birnin, suka kai 15.

A halin yanzu, adadin mutanen da suka kaura zuwa birnin Shenzhen ya dara na sauran biranen kasar Sin, saboda birnin ya bullo da tsarin tabbatar da zamantakewar al'umma a matakai daban daban. Sakataren kwamitin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na birnin Shenzhen Wang Zhongwei ya bayyana cewa, "Mutane su ne mafi muhimmanci, inda mutane dake zuwa birnin Shenzhen, za mu cimma dukkan burinmu. Wannan shi ne taimako mafi muhimmanci ga birnin Shenzhen cikin shekaru 40 da suka gabata, bayan da aka fara bude kofa ga waje. Kwararru a fannoni daban daban da suka zo birnin Shenzhen daga sassan kasar sun tabbatar da bunkasuwar birnin cikin sauri."

A cikin shekaru 40, an raya birnin Shenzhen, inda ya canza daga wani karamin kauye zuwa wani babban birni na zamani mai kunshe da al'umma kusan miliyan 20. Birnin ya cimma nasarori a fannoni da dama da suka hada da raya birane, da harkokin masana'antu da sauransu. Ya kuma dukufa wajen warware matsalar gidajen kwana, wadda ke janyo hankulan dukkan al'umma, kuma ita ce babbar matsala da birnin ya gamu da ita, yayin da ake yin kwaskwarima a kansa.

A lokacin da ya zabi gidan da zai yi haya, bisa shirin gidajen da gwamnatin birnin Shenzhen ya samar domin tallafawa al'umma, Deng Junyao ya yi murna kwarai da gaske, yana mai cewa, "A halin yanzu, farashin gidaje a manyan birane, yana karuwa cikin sauri, ba za mu iya sayan gida ba. Yanzu, na samu gidan da zan zauna bayan shekaru 20 ina aiki a wannan birnin, ina godiya matuka dangane da manufar kyautata zaman al'umma da gwamnatin birnin ta samar."

Haka kuma, birnin ya fito da manufofin ba da gata ga ma'aikatan da suka dawo birnin daga sauran sassan kasar. Misali, samar da hidimar kiwon lafiyar jama'a, da damar samun ilmin tilas ga yaransu, da gidajen kwana ga wadanda suka cika sharadin da aka tanada, har ma ana gaya musu cewa, "Idan har ka zo, to ka zama 'dan asalin birnin."

A watan Yulin bana, an shigar da birnin Shenzhen cikin birane goma mafiya dadin zaman rayuwa tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020. Ko shakka babu birnin Shenzhen ya cancanci yabo.

Burin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje shi ne, kowa zai cimma nasara kamar yadda yake fata. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana yayin taron murnar cika shekaru 40 na aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje. Ya ce, "Ya kamata mu mai da hankali kan bukatun al'umma, domin su more da sakamakon da aka samu a fannonin bunkasuwar tattalin arziki, siyasa, al'adu, zaman takewar al'umma da kyautatuwar muhalli da sauransu. Da kuma, inganta zaman rayuwar karin al'ummomi a dukkan fannoni, ta yadda za su samu wadata." (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China