Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hanyar kawar da talauci ta iyalin Chang Gong
2020-08-27 17:38:14        cri
Chang Gong dake zaune a kauyen Zhaza dake birnin Shannan na jihar Tibet ta kasar Sin ta samu hoton iyalanta ne tana da shekaru 59

Iyalanta duka suna tsaye a falon sabon gidansu, a bayansu kuma, an ajiye wani sabon talibijin da suka saya, a kusa da Chang Gong kuma 'yarsu da mijinta ne suke murmushi, jikokinsu guda biyu suna cike da sha'awar wajen. Gwamnatin wurin ne ta sa aka dauke su wannan hoton bayan sun kaura zuwa sabon gidansu.

Akwai iyalai 480 da suka kunshi mutane 2154 a kauyen Zhaza. A baya Chang Gong tana zaune a tsaunin dake arewacin kauyen kamar sauran mazauna kauyen dake a tudun makiyaya, tsayinsa ya kai sama da mita 4600 daga leburin teku.

An gina gidajen ne da duwatsu da katako, sannan babu isasshen hasken rana,don haka akwai bukatar a kunna fitila a rana.

Yawancin gidajen mazauna kauyen suna kan gangare ne, motoci ba su iya shiga, makaranta da cibiyar lafiya da ma sauransu suna kasan dutsen ne, a kan shafe kusan mintuna 30 kafin a isa wuraren.

Ban da wannan kuma, wutan lantarki a wajen ba shi karfi, a wasu lokuta ma, akan shafe kwanaki biyu zuwa uku babu wutar lantarki. Matsalar da ta fi tsanani ita ce, babu ruwan sha mai tsabta, hakan ya tilastawa mazauna kauyen yin tafiyar kusan mita 500 kafin su samu ruwa.

Lallai,a baya sun sha wahalar rayuwa.

Bisa manufar kawar da talauci ta hanyar kaura zuwa wasu wurare, a watan Janairu na shekarar 2018, kauyen Zhaza ya soma gudanar da aikin kaura zuwa kasan dutse.

An soma aikin gina gidaje a watan Satumba na shekarar 2018, kuma mazauna kauyen sun kaura zuwa sabbin gidajensu a watan Yuni na shekarar 2020, an kwashe shekaru biyu kacal wajen gina sabon wurin kwana, ban da wannan kuma, an kammala ayyukan sanya na'urorin da suka shafi ruwa, wutar lantarki, sadarwa da dai sauransu, kana an gina wani filin shakatawa na al'adu.

Bayan ya kaura zuwa sabon gidansa, karon farko Chang Gong ta zauna a gida mai fadi da kuma haske, kuma ba za ta damu da matsalar rashin wutar lantarki ba, baya ga haka, iyalanta za su sha ruwan famfo a gida. A cewarta, "Zama a nan akwai dadi."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China