Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 45 a Nijar
2020-08-27 19:11:22        cri

Ma'aikatar ayyukan jin kai da shawo kan annoba ta Nijar, ta ce ruwa kamar da bakin kwarya da aka fuskanta a baya bayan nan, ya haddada ambaliyar ruwa a sassan kasar daban daban, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 45, baya ga sama da mutane 226,000 da ambaliyar ta shafa, da kuma gidaje 2,201 da suka lalace.

Babban jami'in ma'aikatar Laouan Magadji, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, yana mai cewa, gwamnati na daukar matakan da suka dace, na ceton rayukan al'ummun da lamarin ya shafa, tare da gyaran madatsan ruwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China