Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An jinkirta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da kungiyoyi masu dauke da makamai
2020-08-28 09:53:22        cri
Mai baiwa shugaban kasar Sudan ta kudu shawara kan harkokin tsaro kana shugaban tawagar shiga tsakanin kan shirin wanzar da zaman lafiya na kasar, Tuk Gatluak, ya sanar a jiya Alhamis cewa, an jinkirta shirin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan ta kudu da kungiyoyi masu dauke da makamai, daga yau Jumma'a 28 ga wata zuwa 31 ga watan na Agusta.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da majalisar rikon kwaryar kasar Sudan ta Kudu ta fitar, Tut ya ce, an jinkirta shirin ne, don tabbatar da cewa, ba a ware wata kungiya ko wani yanki ba.

Gatluk ya bayyana cewa, daga yau har zuwa gobe Asabar, za a ci gaba da aikin bibiyar takardu da suka shafi harkokin tsaro da aka gabatar a yankin Darfur da matakai na siyasa a yankunan kudancin Kordofan da Blue Nile.

Ya kara da cewa, shugaban Sudan ta kudu, Salva Kiir Mayardit, zai yi wa taron sanya hannun da zai samu halartar jami'ai daga Sudan, da ministocin harkokin wajen hukumar raya gwamnatoci dake Afirka (IGAD), da kasashen Chadi, da hadaddiyar daular Larabawa, da Masar da Saudiya jawabi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China