Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 12 sun mutu a hadarin mota a arewa maso yammacin Najeriya
2020-08-28 10:30:25        cri
A kalla mutane 12 ne aka bada rahoton mutuwarsu sakamakon hadarin mota a jihar Zamfara, dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

Faruku Shattima, kakakin jami'iyya PDP na jihar Zamfara, wanda ya tabbatar da faruwar hadarin ga manema labarai a Gusau, babban birninn jihar, ya ce mutanen da suka mutu 'yan jam'iyyarsu ne.

A cewarsa, hadarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Laraba a kan hanyar Tsafe-Gusau dake jjhar.

Kakakin na PDP ya ce, hadarin ya faru ne a lokacin da motar take kokarin iso cikin ayarin gwamnan jihar inda tayi taho mu gama da babbar mota kuma mutanen sun mutu nan take, tuni aka binnesu bisa tsarin islama. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China