Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta kyautata tunaninta game da alakarta da Sin
2020-08-28 20:33:45        cri

A yau Juma'a ne kakakin ma'aikatar wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi kira ga kasar Amurka, da ta kyautata tunanin ta, game da alakar ta da kasar Sin, da ma alakar da sassan biyu suka kulla cikin adalci da sanin ya kamata.

Zhao ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, yana mai cewa, akwai bukatar Amurka ta zanta da bangaren Sin, don shawo kan banbance banbancen su, da bunkasa hadin gwiwa, tare da mayar da alakar sassan biyu kan turba ta gari bisa tsari, da hadin kai da daidaito.

Wasu rahotannin baya bayan nan sun rawaito shugaban Amurka Donald Trump, a yayin babban taron jam'iyyar sa ta Republican, yana cewa idan har aka sake zaben sa matsayin shugaban Amurka, zai tabbatar da kamfanonin kasar sa sun yi kaura daga Sin.

Game da tambaya mai nasaba da wannan batu da aka gabatar masa, Zhao Lijian ya ce, zaben Amurka batu ne na cikin gidan kasar, wanda bai shafi kasar Sin ba. Kuma wannan manufa ce ta Sin da ba ta taba sauyawa ba.

Sai dai kuma jami'in ya ce hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, na samar da gajiya gare su, yayin da fito na fito zai zamo mataki mai cutarwa gare su.

Bugu da kari, Zhao ya ce Sin ta sha alwashin bunkasa hadin gwiwar ta da Amurka, bisa tushen kaucewa tashin hankali, da fito na fito, da fatan sassan biyu za su martaba juna da cin gajiya tare. A lokaci guda kuma, Sin za ta tabbatar da kare ikon ta na mulkin kai, da tsaro da moriyar samar da ci gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China