Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan da Masar da Habasha sun gaza cimma matsaya kan yarjejeniyar gina dam a kogin Nile
2020-08-29 16:09:00        cri

A ranar Juma'a ne kasashen Sudan da Masar da Habasha suka kammala sabon zagayen tattaunawa ba tare da cimma matsaya ba kan batun tsara daftarin yarjejeniyar gina madatsar ruwan Habasha ta GERD a kogin Nile wanda ake sa ran gabatarwa ga kungiyar tarayyar Afrika AU.

A sanarwar da ministan noman rani da albarkatun ruwa na kasar Sudan ya fitar ya ce, kasashen uku sun amince za su kammala tattaunawar da suke gudanarwa a halin yanzu ba tare da an cimma matsaya game da tsara daftarin ba wanda ya kamata a gabatarwa AU a ranar Juma'a.

Sanarwar ta ambato Yasir Abbas, ministan noman rani da albarkatun ruwa na kasar Sudan yana mai cewa, ci gaba da wannan tattanawar da suke a halin yanzu ba lallai ne ta kai ga samun hakikanin sakamako ba.

Ministan na Sudan ya kara da cewa, cimma matsaya lamari ne dake bukatar bin matakan siyasa.

A cewar sanarwar, wakilan kasar Sudan sun jaddada cewa, tattaunawa ce kadai hanyar cimman daidaito, sun ce Sudan a shirye take ta sake dawowa teburin tattaunawar bayan tattaunawa da AU. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China