Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jiragen saman kasa da kasa za su fara zirga-zirga a Ghana
2020-08-31 09:44:27        cri
Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya sanar a jiya cewa, kasar zata dawo da zirga-zirgar jiragen saman kasa da kasa daga gobe, 1 ga watan Augusta, bayan dakatar da su na tsawon watanni 5.

Sai dai shugaban kasar ya ce kafofin shiga kasar na kasa da ruwa, za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Nana Akufo Addo ya bayyana cikin jawabin da ya yi wa kasar cewa, ana bukatar kowanne matafiyi da zai shiga kasar, ya gabatar da sakamakon gwajin da ya yi a wani amintaccen dakin gwaji na kasarsa, dake nuna ba shi da cutar COVID-19.

Ya kara da cewa, za a yi wa kowanne fasinja da zai sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Kotoka, gwajin cutar kan wani farashi da matafiyin zai biya, yana mai cewa za a samu sakamako cikin mintuna 30.

Har ila yau, ya ce gwamnati zata tabbatar da cewa, sassauta matakai a hankali, ciki har da bude filayen jiragen sama, ba su kai ga sake bullar cutar a kasar ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China