Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Afirka na shan matsi a gabar da yawan masu dauke da COVID-19 ya doshi miliyan 1.24
2020-08-31 11:08:39        cri
Cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, ta ce adadin masu dauke da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar ya kai mutum 1,237,070, lamarin da kuma ke kara yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin nahiyar.

Cibiyar Afirka CDC, ta ce kasashe 5 na nahiyar ne ke kunshe da kaso sama da 70 bisa dari na masu fama da wannan cuta, ta kuma bayyana yadda ya zuwa jiya Lahadi, cutar ta hallaka mutum 29,430 a sassan nahiyar.

A bangare guda kuma, baya ga tasirin da cutar ta yi ga fannin kiwon lafiyar al'ummar nahiyar, kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta ce bullar wannan annoba ya haifar da kara durkushewar hanyoyin samar da kudaden shiga na cikin gida a nahiyar.

A cewar kwamishina mai lura da harkokin tattalin arziki, na hukumar zartaswar kungiyar Victor Harison, gwamnatocin kasashen nahiyar na ci gaba da matse bakin aljihu a fannin kasafin kudade, yayin da suke aiwatar da karin matakan ko ta kwana, da dabarun farfadowa, don wanzar da tattalin arzikin kasashen su.

Wasu alkaluma daga kasashe 55 mambobin kungiyar ta AU sun nuna cewa, ma'aunin GDPn kasashen Afirka a bana, zai sauka zuwa tsakanin kasa da maki 4.9 bisa dari zuwa kasa da maki 2.1. An kuma yi hasashen cewa, wannan raguwa za ta kai ta kusan tsakanin dalar Amurka biliyan 135 zuwa biliyan 204, sabanin dala biliyan 2.59 da ake da shi gabanin bullar cutar COVID-19.

A cewar AU, kalubalen da COVID-19 ta haifar, ya kara ingiza matsayin talauci a nahiyar, wanda bankin raya Afirka na AfDB ya yi hasashen zai jefa kusan al'ummar nahiyar, tsakanin mutum miliyan 28.2 zuwa miliyan 49.2 cikin kangin talauci mai tsanani. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China