Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Ghana ya sanar da lokacin bude wasu makarantu
2020-08-31 11:25:01        cri

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sanar da shirin kasar sa, na bude wasu makarantun kasar. Karkashin kwarya kwaryar tsarin bude makarantun, daliban ajujuwa na biyu na karama da babbar sakandare, za su koma karatu tun daga ranar 5 ga watan Oktoba.

Yayin jawabin shugaban kasar na 16 game da halin da kasar ke ciki, don gane da yaki da cutar COVID-19, ya ce an dauki wannan mataki ne domin ba da damar kammala zangon karatu na shekarar 2019 zuwa 2020. An kuma amince da hakan ne, bayan gudanar da shawarwari da ma'aikatar ilimin kasar, da kuma sauran sassan masu ruwa da tsaki.

Shugaban na Ghana, ya kuma ce makarantun renon yara, da na firamare, da 'yan ajujuwan farko na sakandare, za su kasance a rufe har zuwa watan Janairun shekara mai zuwa.

An dai rufe daukacin makarantun kasar ta Ghana ne tun a ranar 16 ga watan Maris din da ya gabata, bayan da aka gano masu dauke da cutar a kasar kwanaki 4 gabanin hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China