Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ba ta da ikon tilastawa kasar Sin tsarin siyasar da ta zabi
2020-08-31 20:10:58        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana cewa, al'ummar Sinawa sun riga sun san cewa, tsarin gurguza mai sigar musamman na kasar Sin yana da kyau ko a'a. A don haka, ba 'yan siyasar Amurka ne za su fada musu kyau ko rashin kyau wannan tsarin ba.

Zhao Lijian ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai da aka shirya Litinin din nan. Yana mai cewa, a matsayinta na babbar kasar dake huldar cinikayya da sama da kasashe da yankuna 130, ci gaban kasar Sin wata dama ce ko barazana ga duniya? za kuma a iya samun amsa daidai daga irin musaya da hadin gwiwar kasar Sin da sauran kasashe.

Rahotanni na cewa, a baya-baya nan mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro Robert O'Brien, ya bayyana cikin wata zantawa da hukumar Atlantic, inda ya zargi kasar Sin kan wasu batutuwa da suka shafi tsarin siyasar kasar ta Sin, da batutuwan Taiwan, da Hong Kong, da tekun kudancin kasar Sin. Har ma ya ikirarin amfani da tsarin kawance na Amurka wajen tunkarar kalubalolin da kasarsa ke fuskanta daga Sin da Rasha. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China