Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatan Lafiya Na Kasar Sin Za Su Yi Mu'alama Da Takwarorinsu Na Guinea
2020-08-31 20:31:26        cri

Zhao Lijian, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin cewa, ma'aikatan lafiya na kasar Sin sun kammala aikinsu a kasar Sudan ta Kudu, sun riga sun isa kasar Guinea kwanan baya, kuma za su yi mu'amala da takwarorinsu a kasar.

Yayin da kakakin yake amsa tambayar da aka yi masa a wajen taron manema labaru da aka saba shiryawa a Beijing, ya yi karin bayanin cewa, ma'aikatan lafiyar kasar Sin za su shafe kwanaki 10 suna aiki a Guinea, inda za su ziyarci wasu wurare, shirya taron bita da ba da aikin horo don yin musayar fasahohin dakile da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, a kokarin ba da taimako wajen inganta karfin 'yan kasar Guinea wajen yaki da annobar. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da Guinea da sauran kasashen Afirka wajen yaki da annobar don ganin bayanta cikin hanzari. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China