Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da tsarin kara fadada gwajin COVID-19
2020-09-01 10:50:16        cri

Wani tsarin aiki da mahukuntan kasar Sin suka fitar, ya nuna irin tanadi da aka yi, na fadada ayyukan gwajin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 a cikin kasar.

Kundin bayani game da tsarin, wanda majalissar gudanarwar kasar ta fitar ya nuna cewa, za a kafa dakunan gwajin cutar guda 100 a sassan kasar daban daban, inda ko wane daya daga dakunan gwajin, zai iya karbar samfur na mutane 10,000 a duk rana.

Kaza lika kundin ya jaddada muhimmancin karfafa gwiwar dakunan gwaji masu zaman kan su, ta yadda za su shiga aikin gwajin wannan cuta, bisa tanajin dokokin gwamnati na samar da hidima mai inganci.

Kundin ya kuma bayyana hakan a matsayin hanya, wadda za ta taimaka wajen cimma nasarar gwada dukkanin mazauna unguwanni cikin kwanaki 5 zuwa mako daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China