Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara farfado da tattalin arzikin Sin
2020-09-01 10:51:28        cri

Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar a jiya, an ce, yawan alkaluman sayar da kayayyaki na kamfanonin kasar ko PMI na watan Agusta, ya kai kaso 51 cikin dari. Karin sama da kaso 50 na nuna fadadar alkaluman, kasa da 50 kuma na nuni ga raguwar su. Yanzu dai an shafe watanni 6 a jere alkaluman na PMI na kasar Sin na karuwa. Bisa kididdigar, an farfado da aikin samar da kayayyaki da bukatun cikin gida, wanda hakan ya shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai kara samun farfadowa.

Wani jami'in hukumar kididdiga ta kasar Sin ya bayyana cewa, yawan bukatun cikin gida ya ci gaba da karuwa, dangantakar da ke tsakanin samarwa da bukatu na samun kyautatuwa sannu a hankali. Kana yawan kayayyakin da ake bukata don fitar da zuwa kasashen waje na karuwa, baya ga yadda kasuwanni ke samun farfadowa, yayin da kamfanoni ke kara imaninsu ga cinikayya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China