Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen tashe tashen hankula da 'yan adawa
2020-09-01 12:48:03        cri

Gwamnatin rikon kwarya a kasar Sudan, da bangarorin 'yan adawar kasar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar wasu sassan kasar cikin gwamman shekaru.

A jiya Litinin ne dai aka rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Juba, fadar gwamnatin Sudan ta kudu mai makwaftaka da Sudan din. Ana kuma sa ran hakan zai kawo karshen yake-yake da ake fama da su, a yankunan Darfur, da kudancin Kordofan da kuma jihar Blue Nile.

Da yake tsokaci yayin sanya hannu kan wannan yarjejeniya, shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce matakin zai haifar da dawowar zaman lafiya da tsaro a Sudan.

Gwamnatin Sudan ta cimma daidaito da gungun sassan 'yan adawa karkashin hadakar SRF, wadda ta kunshi kungiyar SPLM-N dake karkashin jagorancin Malik Agar, da kungiyar JEM karkashin jagorancin Jibril Ibrahim, da DUP ta Eltom Hajou. Sai kuma SLM dake karkashin jagorancin Minni Minnawi.

Yarjejeniyar dai ta kunshi rabon iko, da albarkatu, da adalci wajen mika mulki, da wanzar da tsaro, da lura da bukatun 'yan kasar da suka rasa matsugunnan su a cikin gida, da ma masu gudun hijira a wajen kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China