Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya zanta da sarkin Morocco ta wayar tarho
2020-09-01 13:06:11        cri
Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da sarkin kasar Morocco Sidi Mohammed.

A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya mika gaisuwa da goyon baya ga gwamnati da jama'ar kasar Morocco, game da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Xi Jinping ya ce, annobar cutar COVID-19 ta kasance babban kalubale ga kasa da kasa, kuma ya sake jaddada cewa, bayan Sin ta samu allurar rigakafi, za ta gabatarwa sassan kasa da kasa, kuma, da farko za ta baiwa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.

Ya ce, kasar Sin tana fatan inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, a fannin inganta shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, da tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa.

A nasa bangare kuma, Sidi Mohammed ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, kasarsa tana bunkasa cikin yanayi mai kyau, bisa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin. Kaza lika kasar Morocco tana daukar Sin a matsayin wadda ke kan gaba, ta fuskar habaka hadin gwiwa, tana kuma goyon bayan kasar Sin wajen kare 'yancin kanta, da kiyaye tsaro da babbar moriyar kasa yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China