Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Bankin Duniya da ya nuna kwarewar aiki da martabar yanayin kasuwanci na duniya
2020-09-01 20:11:18        cri
Kasar Sin ta bukaci Bankin Duniya da ya gudanar da bincike na cikin gida ta hanyar nuna adalci da gaskiya da yin komai a bayyane, kamar yadda dokoki da ka'idoji na hukumomin bangarori daban-daban suka tanada.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ita ce ta bayyana haka Talatar nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa. Tana mai cewa, kasar Sin za ta kare martabar bankin da kasashe mambobinsa, da kiyaye kwarewar aiki da martabar yin kasuwanci na kasa da kasa.

Wasu rahotanni na nuna cewa, bankin duniya ya fitar da wani bayani cewa, wasu ma'aikatansa sun jirkita matsayin kasashe game da tafiyar da harkokin kasuwanci a duniya, kuma akwai yiwuwar za a jinkira fitar da jeren sunayen. An kuma fahimci cewa, yadda aka jirkita matsayin kasashen ya shafi kasar Sin da sauran kasashe. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China