Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsarin diflomasiyar Amurka abin takaici ne ga kasar da ma barazana ga duniya
2020-09-01 20:35:33        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying, ta bayyana yayin taron manema labarai da aka shirya Talatar nan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cewa, tsarin diflomasiyar Amurka a yau abin takaici ne, ya zama tsarin hadin baki da sanya takunkumi, da karya da kuma dora laifi ga wani.

A kwanakin baya ne, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka David R. Stilwell ya bayyana cewa, a baya-bayan nan Amurkar ta gudanar da wasu sauye-sauye a manufofinta, sakamakon karuwar barazana daga kasar Sin. Da take mayar da martani kan wannan tambaya, Hua, ta ce kalaman da Mr. Stilwell ya yi, karya ce tsagwaronta, kuma wasu manyan jami'an diflomasiyar Amurka sun sha yin karairayi, da yada jita-jita da bata sunan kasar Sin da furta kalaman da ba su dace ba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China