Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta raya kanta yadda ya kamata yayin da take dakile da kandagarkin annobar COVID-19
2020-09-01 21:14:17        cri

Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Talata a nan Beijing cewa, a watan Agustan bana, bukatun da ake da su a fannin kera kayayyaki suna ci gaba da farfadowa a kasar Sin, inda kuma ake kyautata samun daidaito tsakanin abubuwan da ake samarwa da bukata, kana an gaggauta farfado da ayyukan ba da hidima. Kasar Sin ta raya kanta yadda ya kamata yayin da take dakile da kandagarkin annobar COVID-19. Madam Hua ta jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da habaka bukatun cikin gida, da kara bude kofa ga ketare, a kokarin ganin ci gaban kasar ya kara azama kan bunkasar duniya baki daya, tare da kara samar wa kasashen duniya damammaki. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China