2020-09-02 09:56:09 cri |
Shugaban hukumar ta GFA Kurt Okraku, ya yi kira da a samar da hadin kai tsakanin 'yan kwallo da sassan masu ruwa da tsaki, domin inganta harkar wasan a kasar. Mr. Okraku ya ce, kwallon kafa na da matukar karbuwa a Ghana, kuma wasa ne daya tilo dake hade kan al'ummar kasar, don haka ya zama wajibi, a yi aiki tukuru wajen habaka shi, ta yadda zai samar da wadata ga kowa.
Jami'in ya kara da yin kira ga dukkanin sassa, da su hada karfi da karfi wajen gina wasan kwallo mai nagarta a kasar.
Muhimman kudurori da aka tattauna kan su yayin taron na GFA, sun hada da batun kakar shekarar 2019-20 da aka soke, bayan bullar cutar COVID-19. Kana an amince da bude sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 a watan Oktoba dake tafe, muddin dai gwamnatin kasar ta dage dakatarwar da ta yiwa harkokin wasannin kasar. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China