2020-09-02 11:08:49 cri |
A cewar rahoton kwamitin sulhun MDD, an zabe Nijer domin ta jagoranci taruka 4 wadanda zasu bayar da fifiko kan wasu muhimman bangarori, manufar hakan shi ne, domin aiwatar da tsarin ayyukan kwamitin sulhun bisa gaskiya da inganci.
Jadakan jamhuriyar Nijer a MDD yace, hakika, tsarin diflomasiyya shine lalibo hanyoyin daidaita al'amurra, jakadan ya amsa tambayoyi da suka hada da batun hadaddiyar yarjejeniyar nan ta JCPA, wato yarjejeniyar nukiliyar Iran, ita dai wannan yarjejeniyar ta shirin makaman Iran wacce aka cimma matsaya kanta a birnin Vienna a ranar 14 ga watan Yulin shekarar 2015, tsakanin kasar Iran da wakilan mambobin kasashe 5 masu kujerun dindindin a MDD da suka hada da Sin, Faransa, Rasha, Birtaniya da Amurka sai kuma Jamus da kungiyar tarayyar Turai. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China