Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mazauna yankin HK dubu 126 sun yi gwajin cutar COVID-19
2020-09-02 14:24:07        cri

Mai magana da yawun gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ya bayyana a daren jiya Talata cewa, an fara aikin gwajin kwayar cutar COVID-19 a unguwannin yankin daga ran 1 ga wata, kuma ana gudanar da wannan aiki yadda ya kamata a unguwanni 141, yayin da yawan mazauna unguwannin da suka yi gwaji ya kai dubu 126.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a kwashe kwanaki 7 ana gudanar da wannan aiki, kuma idan da bukata za a iya tsawaita wa'adin aikin da kwanakin da ba za su dara 7 ba. Bisa tsarin aikin, mutane za su iya yin gwajin bisa radin kansu ba tare da biyan kudin ba, don gano wadanda suka kamu da cutar, da ma kebe su, da jiyyarsu tun a kan lokaci.

(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China