Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kyautata zaman rayuwa a birnin Tianjin
2020-09-02 15:58:11        cri

A shekarun baya baya nan, kauyen Qianjin ya taba kasancewa wuri mafi talauci a garin Beizhakou dake kudancin birnin Tianjin. A shekarar 2017, an kyautata tsarin kamfanoni fiye da dubu 20, don haka aka rufe kamfanoni mafi kankanta, wadanda ba su kai ma'auni ba a kauyen.

A shekarar bara, a sakamakon raya sha'anin noma ba tare da gurbata yanayi ba, da sha'anin yawon shakatawa a kauyen, yawan kudin shiga na ko wane mutum a kauyen ya zarce dubu 27.

A halin yanzu, kauyen Qianjin ya kansance kamar koriyar ganuwa, da fadinta ya kai muraba'in kilomita 736, wadda ke a tsakanin cibiyar birnin Tianjin da sabon yankin Binhai na birnin.

A lokacin da, ana gudanar da ayyukan otel da na yawon shakatawa da dama a kauyen, inda a ko wace shekara, masu yawon shakatawa kimanin dubu 350 ke shiga kauyen, wanda hakan ke gurbata muhallin kauyen sosai.

Tun daga shekarar 2017, Tianjin ya kara zuba jari, da yin kokarin sa kaimi ga farfado da fadamar dake kauyen. Ana kuma ta yin kokarin neman moriyar jama'a, da daidaita matsalolin jama'a. A cikin wasu shekaru da suka gabata, birnin Tianjin yana kokarin kara samar da aikin yi, da daga kudin shigar jama'a, da kara tabbatar da inshorar kula da tsofaffi da samar da hidimar likitanci.

Kaza lika birnin na kara taimakawa jama'a dake cikin mawuyacin hali da dai sauransu. A shekarar 2019, yawan kudin shiga na mazaunan birnin Tianjin ya zarce Yuan dubu 40, wanda ya kai matsayi na hudu a duk kasar Sin. Kana yawan shekarun haihuwar mazaunan birnin ya zarce kwatankwacin yawansa a dukkan kasar Sin.

Ana samun babban canji a birnin Tianjin, da ci gaba mai inganci, kuma birnin yana da kyakkyawar makoma a nan gaba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China