Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin majalisar kafa dokokin Amurka: Jami'an kasar sun boye bullar COVID-19
2020-09-02 20:55:17        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyanawa taron manema labarai da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing Larabar nan cewa, ba ta son fadi kome ba kan matakin Amurka na addabar barkewar cutar COVID-19, amma alkaluman da kasar ta fitar, ba za su rudi mutane ba.

Rahotanni na cewa, kwamitin musamman na majalisar wakilan kasar game da binciken yadda gwamnatin kasar Amurka take dakile cutar COVID-19, a kwanakin nan ya fitar da wata takardar bayani, inda ya bayyana cewa, sanarwoyin da jami'an gwamnati suka faitar, bai su yi daidai da hakikanin abubuwan dake cikin rahotannin da aka bayar, kuma da gangan ne sun boye bayanai game da annobar, abin da ya haddasa mutuwar karin mutane fiye da dubu 58 tun a watan Yuni, baya ga miliyoyin Amurka da annobar ta cusa rayukansu cikin hadari. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China