Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya ziyarci kasashen Turai ne domin tuntubar juna
2020-09-02 21:13:52        cri

Yau ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyararsa a kasashe 5 na Turai. Wasu kafofin yada labaru sun ce, dalilin da ya sa Wang Yi ya yi wannan ziyara, shi ne domin neman samun goyon baya a kasashen Turai.

Dangane da hakan, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Laraba a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a Beijing cewa, wadannan kalamai ba haka ba ne. Dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin ya ziyarci kasashen 5 na Turai shi ne domin tuntubar su dangane da manyan tsare-tsare, yayin da rashin tabbas yake karuwa a duniya. Kasashen Sin da Turai sun cimma daidaito kan ko za a bi manufar cudanyar sassa daban daban ko kuma ra'ayi na kashin kai, ko za a bude kofa ko kuma rufe kofa, ko za a yi hadin gwiwa ko kuma za a yi adawa da juna da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China