2020-09-02 21:44:28 cri |
Da farko, shugaban ya ce sabon yanayin da duniyarmu ke ciki, ya haifar da kalubaloli gami da damammakin samun ci gaba. Idan har muna bukatar raya tattalin arziki, akwai bukatar yin amfani da damammaki, gami da magance wasu kalubaloli.
Na biyu, shugaban ya jaddada muhimmancin ganin fannoni daban daban na tattalin arziki sun gudana kamar yadda ake bukata, ta yadda za a tabbatar da ingancin kasuwannin cikin gida, da taimakawa raya harkar ciniki tare da sauran kasashe.
Na uku, Xi Jinping ya ce dole ne a yi matukar kokarin raya kimiyya da fasaha, ta yadda za a samu damar raya wasu bangarori masu nasaba da fasahohin zamani, da taimakawa raya tattalin arziki.
Na hudu, a cewar shugaban kasar Sin, za a rika zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar, don kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa, da daidaita matsalolin da za su iya kunno kai yayin da ake kokarin raya kasa.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China