Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi yace Sin a shirya take tayi aiki da Rasha don kiyaye sakamakon nasarorin yakin duniya na II
2020-09-03 09:50:17        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar cewa a shirye yake yayi aiki da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, domin yin aiki tare da kasashen duniya wajen tabbatar da kiyaye babbar nasarar da aka samu a yakin duniya na biyu wato WWII, da kuma tabbatar da daidaito da adalci.

A musayar sakonnin da suka yi da Putin domin bikin murnar cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen WWII, Xi ya bayyana cewa, haka ma batun yake an cika shekaru 75 ke nan da samun nasarar Sinawa na kawo karshen yakin cin zali na harin Japanawa da yakin tarayyar Sabiya kan Japanawa wanda ya tabbatar da samun nasarar kawo karshen yakin cin zali a duniya.

A matsayinsu na kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Xi ya jaddada cewa Sin da Rasha dukkanninsu suna daukar muhimman nauyi dake bisa wuyansu domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban duniya.

Ya ce a shirye yake ya yi aiki da Putin wajen amfani da nasarar cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen nuna adawa da hare haren cin zali na duniya a matsayin wata muhimmiyar dama da za ta yiwa kasashensu jagoranci wajen zurfafa yin hadin gwiwa da juna.

Ya kuma jaddada cewa bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa da kasa da kasa domin tabbatar da aiwatar da tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban, da kuma gina tsarin makoma mai inganci ga dukkan bil adama, domin baiwa al'ummomi masu zuwa a nan gaba damar more rayuwa cikin yanayin zaman lafiya mai dorewa, da samar da tsaro na bai daya, da kuma kyakkyawar makoma gare su.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China