Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Birtaniya: Yakin kin jinin Japanawa na Sin ya taka babbar rawa a nasarar yakin kin tafarkin murdiya na duniya
2020-09-03 11:10:15        cri

A bana ne ake cika shekaru 75, tun bayan da al'ummun Sinawa suka yi nasarar yakin kin jinin Japanawa, kuma ita ce shekarar cika shekaru 75 da al'ummun kasa da kasa suka yi nasarar yakin kin tafarkin murdiya, don haka bai kamata ba a manta da tarihi ba, kuma ya dace a koyi darasi daga tarihi, ta yadda za a kara darajanta zaman lafiyar da ake shimfida.

Masanin harkokin kasar Sin na jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya Rana Mitter, ya bayyana cewa, yakin kin jinin Japanawa da al'ummun Sinawa suka yi, ya taka babbar rawa a fannin cimma nasarar yakin kin tafarkin murdiya da al'ummun kasashen duniya suka yi.

A kwanakin baya bayan nan ne, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta jami'ar Oxford ta Birtaniya Rana Mitter, ya zanta da wakilinmu na CMG, inda ya bayyana cewa, yakin kin jinin Japanawan da al'ummun Sinawa suka yi, ya taka babbar rawa kan nasarar yakin kin tafarkin murdiya da al'ummun kasashen duniya suka yi, kuma makasudin yin nazari kan tarihin yake-yaken shi ne, gujewa sake barkewar yaki, da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya.

Farfesa Mitter ya taba rubuta wani littafi mai taken "Kasar Sin, aminiya ce da aka taba mantawa da ita", inda ya rubuta wasu labarai da suka faru a filin fagen kasar Sin.

Farfesa Mitter ya gaya wa wakilinmu cewa, yawancin masu karanta littafin na kasashen yamma, sun yi mamaki matuka yayin da suke karanta labaran dake cikin littafin, saboda ba su fahimci tarihin kasar Sin a wancan lokaci ba ko kadan, amma bayan da suka gano sojoji da al'ummun Sinawa sama da miliyan goma, wadanda suka yi yaki da kusan daukacin sojojin kasar Japan sun rasa rayuka a yakin kin jin Japanawa, sun rika fahimtar cewa, kasar Sin ta taba taka babbar rawa kan nasarar da aka yi, a cikin yakin duniya na biyu, yana mai cewa, "Ina ganin cewa, yawancin al'ummun kasashen yamma ba su gane cewa, kasar Sin ta taba taka muhimmiyar rawa a yakin duniya na biyu ba, amma idan kana son kara fahimtar lamarin, dole ne ka dubu al'amuran da suka faru a shekarar 1938, don gano wane namijin kokari kasar Sin ta yi a filin daga. Hakika a wancan lokaci, masu nazarin harkokin yau da kullum, ciki har da wasu jami'an diplomasiyya na kasashen yamma, sun dauka cewa, ba zai yiwu kasar Sin ta doke kasar Japan ba, saboda a bayyana Japan ta fi ta karfi. Wato dai Sin ba ta da zabi illa ta mika wuya. Amma abun mamaki shi ne, sojojin kasar Sin, da al'ummun Sinawa sun ci gaba da gwabza yaki da sojojin Japan har suka yi nasara."

Farfesa Mitter ya kara da cewa, alkaluman nazari sun nuna cewa, yakin kin jinin Japanawan da al'ummun Sinawa suka yi, ya taka muhimmiyar rawa kan nasarar yakin kin tafarkin murdiya da al'ummun kasashen duniya suka yi, a cewarsa: "Idan da sojojin kasar Sin, da al'ummun Sinawa ba su ci gaba da yin yaki da sojojin Japan tsakanin shekarar 1937 zuwa 1941 ba, da zai yi matukar wahala a yi nasarar yaki a Asiya da Turai. Kila ma zai yi wahala a yi nasarar kin tafarkin murdiya a fadin duniya. Shi ya sa ana iya cewa, yakin kin jinin Japanawa na kasar Sin, yana da babbar ma'ana ga nasarar yakin kin tafarkin murdiya na duniya."

Farfesa Mitter ya yi nuni da cewa, ma'anar waiwayi tarihin yakin duniya na biyu ita ce, kaucewa sake barkewar yaki, tare kuma da kiyaye huldar kasa da kasa mai zaman karko, yana mai cewa, "A ganina, ma'anar waiwayar yakin duniya na biyu ita ce, hana sake barkewar yaki, saboda tarihin yakin ya ba mu wannan gargadi, kana daga darasin da muka koya daga yakin duniya na biyu, muna iya kara gano cewa, ya kamata a kara kafa wani tsarin kasa da kasa na hadin hai da hadin gwiwa. alal misali, MDD da aka kafa, tana taka babbar rawa wajen kiyaye huldar kasa da kasa mai zaman karko, tun bayan yakin duniya na biyu."

Haka zalika, farfesa Mitter ya nuna cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, masanan ilmin tarihi na kasashen duniya, suna kara mai da hankali kan rawar da kasar Sin ta taka a cikin yakin duniya na biyu, har ma wasu masanan Amurka su ma sun fara yin nazari, kan boren da aka yi a gadar Lugouqiao dake birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 1937, yana mai cewa, "A cikin shekaru goma da suka gabata, masanan ilmin tarihi na kasashen duniya, suna kara ba da muhimmanci kan rawar da kasar Sin ta taka a yakin duniya na biyu. Misali, masanin Amurka Richard Frank, ya rubuta wani sabon littafi a bana, inda ya yi bayani kan tarihin yakin tekun Pasifik, a cikin littafin, ya fara ne daga boren da aka yi a gadar Lugouqiao dake birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 1937, a maimakon harin da aka kai tashar tekun Pearl ta Amurka a shekarar 1941. Wannan muhimmiyar shaida ce da ta nuna cewa, masanan duniya sun fara yin nazari kan amfanin kasar Sin a yakin duniya na biyu."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China