Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon tsarin fasahar kasar Sin ba ya hari wani takamammen kamfani
2020-09-03 20:14:34        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana cewa, sabbin canje-canje da aka yiwa wasu tsarin fasahohin kere-kere na kasar, da ka iya fuskantar haranci ko takaita fitar da su zuwa kasashen ketare, bai saba ka'idojin kasa da kasa ba, kuma ba sa harin wani takamammen kamfani.

Gao Feng, wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ma'aikatarsa ta kira Alhamis din nan, ya ce, daga matsayin tsarin, wanda shi ne irinsa na farko tun a shekarar 2008, abu ne da aka saba ingantawa, bisa ci gaban kimiyya da fasaha, da kuma bukatar inganta musanya da hadin gwiwar harkokin kimiyya da fasahar kere-kere na kasa da kasa. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China