Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na dakon sakamakon gwaji game da mutuwar giwaye 22
2020-09-04 11:27:53        cri
Mahukunta a Zimbabwe, sun ce har yanzu suna dakon sakamakon gwajin da ake yiwa gawawwakin wasu giwaye 22 da suka mutu, a wasu gandayen dajin kasar masu tsaro.

Ministan ma'aikatar muhalli, yanayi, da harkokin yawon shakatawa na kasar Mangaliso Ndlovu, ya ce an gano gawawwakin giwayen ne kusa da babban dajin Hwange dake kasar.

Mr. Bdlovu ya kara da cewa, mafi yawan giwayen da suka mutu matasa ne, ana kuma nazari game da dalilin mutuwar su a wani dakin bincike dake Victoria Falls. Ya ce kawo yanzu ba a kammala gwaje gwajen ba, amma dai an kawar da yiwuwar cewa, gubar anthrax ce ta hallaka su.

Wasu alamu sun nuna cewa, mai yiwuwa wasu tsirrai masu dauke da kwayoyin cutar bacteria ne suka sabbaba rasuwar giwayen, sai dai kuma masu gwaje gwajen, ba su karfafa wannan hasashe ba, suna masu fatan tantance dukkanin shaidu, kafin fitar da sakamakon gwaje gwajen nasu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China