Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na Sin na 2020
2020-09-04 14:47:20        cri

An bude bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki a birnin Beijing. A matsayin bikin dake kan gaba a wannan fanni, wannan shi ne bikin cinikayyar kasa da kasa mafi muhimmanci da kasar Sin ta gudanar a fili, kuma karo na farko, bayan ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Mataimakin magajin garin birnin Beijing Yang Jinbai ya bayyana cewa, a wannan karo, za a gudanar da taron kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa, da dandalin tattaunawar shugabanni guda hudu, da tarukan tattauna sana'o'in ba da hidima da kuma tarukan kwararru sama da guda 100, da sauran aikace-aikace da dama.

Haka kuma, ya ce, bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na bana ya hada harkokin bikin baje kolin al'adu, da na bikin baje kolin yawon shakatawa, da sha'anin kudi, da wasannin Olympics na lokacin sanyi, da na mutum-mutumin, da sauransu.

A sa'i daya kuma, za a gudanar da taro a fili da kuma ta kafar bidiyo, ta yadda mahalarta taron da 'yan kasuwan kasashen ketare za su halarci taron ba tare da wata matsala ba. Galibin mahalarta taron dake kasar Sin za su halarci tarukan da abin ya shafa da kansu, kana, ban da wasu dandalin nune-nunan da aka kafa cikin dakuna, an kuma kafa wasu dandalin nune-nune a fili. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China