Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi na fatan a hada karfi da karfe don yayata ci gaban cinikayyar ba da hidima tsakanin kasa da kasa
2020-09-04 21:09:47        cri

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yiwa bakin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin shekarar 2020 da aka bude a birnin Beijing jawabi.

A jawabin nasa wanda ya gabatar da kafar bidiyo, Shugaba Xi ya yi kira da a hada karfi da karfe, don magance matsaloli, ta yadda za a yayata ci gaba, da makoma ga cinikayyar ba da hidima ta kasa da kasa da hanzarta farfado da tattalin arzikin duniya.

Xi ya kuma yi nuni da cewa, bude kofa da yin hadin gwiwa a fannonin samar da hidima ga jama'a na kara zama wani muhimmin karfi na samun ci gaba. Xi Jinping ya kuma gabatar da shawarar kara bude kofa, da samar da yanayin hadin gwiwa mai dacewa. Ya kuma yi kira ga dukkan kasashen duniya, da su yi aiki tare, don ingiza hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkre, haka kuma kasashe su yi aiki tare, don bullo da wani sabon yanayi na hadin gwiwar moriyar juna.

Shugaba Xi, ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kafa kawance a fannin cinikayyar ba da hidima ta kasa da kasa. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China