Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya jaddada muhimmancin kasashen BRICS game da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya
2020-09-05 16:10:53        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce, kamata ya yi mambobin kasashen BRICS su kara himma, da zurfafa hadin gwiwa, da karfafa aiki tare domin sauke nauyin dake bisa wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da cigaban kasa da kasa.

Wang, yayi wannan tsokaci ne a lokacin da ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen mambobin BRICS a ranar Juma'a ta kafar bidiyo.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, shine ya jagoranci taron. Ministan harkokin wajen Indiya Subrahmanyam Jaishankar, da na Afrika ta kudu Naledi Pandor, da ministan harkokin wajen Brazil Ernesto Araujo duka sun halarci taron.

Wang yace, a halin yanzu, duniya na fuskantar jerin sabbin matsaloli da kalubaloli: daga ciki, annobar COVID-19 ta haifar da mummunar barazana kai tsaye ga lafiyar bil adama, nuna ra'ayin kashin kai yana kara zama babban kalubale ga cudanyar kasa da kasa, kana nuna kariyar ciniki tana ci gaba da kasancewa matsalar dake shafar makomar tattalin arzikin duniya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China