Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'i: Akwai makoma mai haske dangane da hadin gwiwar da ake yi tsakanin Kenya da Sin a fannin ayyukan hidimomi
2020-09-05 17:41:37        cri
A jiya Juma'a, an bude bikin bajekolin hadar hadar ayyukan hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda jami'i mai kula da aikin fitar da kayayyaki na kasar Kenya Wilfred Marube, wanda ya halarci bikin, ya fadawa wakilin CRI cewa, yana sa ran ganin makoma mai haske dangane da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Kenya da Sin a fannin hada hadar ayyukan hidimomi.

A cewar mista Marube, kasar Sin daya ce daga cikin manyan abokan huldar kasar Kenya ta fuskar ciniki, sa'an nan kasar Kenya tana dora muhimmanci sosai ga aikin sayar da kayayyaki a kasuwar kasar Sin. A ganinsa, damar halartar bikin cinikayyar hidimomi a wannan karo ta sanya kasar Kenya kara lura da ciniki a wannan fanni, wadda kuma ke samar da cikakkun damammakin hadin gwiwa ga kamfanoni masu kula da ayyukan jinya, da sadarwa, da jigilar kaya, da bankuna, da inshora, da makamantansu. Ta la'akari da yadda annobar COVID-19 ke haifar da tsaiko ga kasuwanci da cinikin kasa da kasa, hada hadar ayyukan bada hadimomi zai iya taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, musamman ma bayan da aka samu shawo kan cutar, in ji jami'in na kasar Kenya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China