Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abu Ne Mai Sauki Ga Kasa Ta Sayi Hatsi Daga Ketare, Amma Zai Yi Wuya Ta Iya Tsayawa Da Kafarta
2020-09-10 10:05:54        cri

Kwanan baya, shugaban kasar Sin ya yi kira ga dukkan al'ummomin kasar da su yi tsimin abinci. Wasu sun ce, idan ba mu da isasshen abinci, to, mu saya daga kasashen ketare, inda farashin hatsi ya yi kasa da na kasar Sin. Har ma wasu masanan ilmin tattalin arziki sun taba yin kiran a gina masana'antu kan dukkan gonakin da ke kasar Sin don raya tattalin arziki, saboda a ganinsu, sayen abinci daga ketare zai ishe al'ummomin Sin sosai.

To, idan manoma ba su ci gaba da ayyukan gona ba, al'ummomin Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 ko fiye da haka, suka dogara da abincin da ake saya daga ketare, me zai faru a kasar Sin ke nan? Sanin kowa ne cewa, idan wata kasa ta dogara da sayen abinci daga ketare, to, sannu a hankali wannan kasa za ta fada hannun 'yan jari hujja na kasashen waje, za ta bi umurninsu, ba za ta iya tsayawa da kafafunta ba. Wasu sun ce, a'a, ba zai yiwu ba, a zaburar da mutane kawai. Batun sayen abinci daga ketare ba shi da nasaba da samun ikon mulki kan wata kasa. To, bari in yi karin bayani.

Idan wata kasa ta fara sayen dukkan abinci daga kasashen ketare, kuma ba ta goyi bayan manomanta wajen yin ayyukan gona ba, to, manoma suka daina ayyukansu, a kwana a tashi gonakin za su lalace, ba za su dace da noma ba. Idan yake-yake ko bala'u daga indallahi sun faru, to, farashin abinci zai karu kwarai da gaske a duk duniya. Wannan kasa ba za ta iya samarwa al'ummominta isasshen abinci bisa ga karfinta ba, ba yadda wannan kasa za ta yi, sai ta sayi abinci mai matukar tsada daga kasashen ketare, wato ta sayi abinci mai matukar tsada daga hannun 'yan jari hujja masu kwadayi da son kai. Wadannan 'yan jari hujja ba su yi ayyukan jin kai ba, dole ne su gabatar da wasu sharudda domin samun karin riba. Sannu a hankali, 'yan jari hujjar kasashen waje suna iya kutsa kai cikin harkokin wannan kasa ta hanyar sayar mata da abinci. Wannan kasa ba za ta iya yanke hukunci da kanta ba, kana ba za ta iya tsayawa da kafafunta ba. Ma iya cewa, abu ne mai sauki kasa ta sayi hatsi daga ketare, amma da wuya ta iya tsayawa da kafafunta. Idan aka dogaro da sayen abinci daga ketare domin samun isasshen abinci, to, barazanar da za a fuskanta tana iya zarce tsammanin mutane. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China