Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hambararren shugaban Mali Keita ya tafi UAE neman lafiya
2020-09-06 16:08:26        cri
Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar Mali wanda sojojin kasar suka yi wa juyin mulki a watan Ogasta, da yammacin ranar Asabar ya tafi zuwa birnin Abu Dhabi, na hadaddiyar daular larabawa UAE, domin a duba lafiyarsa, wata majiyar jami'an tsaro ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jami'in tsaron wanda ya nemi a sakaye sunansa, yace, Keita ya tashi daga birnin Bamako ne cikin wani jirgin saman da aka dauki shatarsa, wanda aka tura daga UAE, kuma ana tsammanin zai shafe kwanaki 10 zuwa 15 a Abu Dhabi.

A cewar kafafen yada labaran cikin gidan kasar, Keita ya samu rakiyar mai dakinsa da likitocinsa.

Tsohon shugaban na Mali mai shekaru 75 a duniya, tun da farko cikin wannan mako an kwantar da shi a wani asibiti mai zaman kansa sakamakon lalurar shanyewar barin jiki.

Kungiyar fafutukar ceto al'ummar kasar ta CNSP, wacce ke jan ragamar kasar a halin yanzu, ta sanar a ranar 27 ga watan Ogasta cewa, ta saki hambararren shugaban kasar ta Mali, wanda ake tsare da shi a wani sansanin sojojin kasar.

An saki Keita ne bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin CNSP da wakilai masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS, wadanda suka zauna a kasar tsakanin 22-24 ga watan Ogasta.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China