Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin zai halarci taron yabawa jaruman kasar a yaki da annobar COVID-19
2020-09-06 16:20:56        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron yabawa jaruman kasar da suka nuna bajimta wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Za a gudanar da taron da safiyar ranar Talata mai zuwa a birnin Beijing.

Xi, wanda kuma shine babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta sojojin kasar, zai bayar da lambobin yabo ga jaruman, kana zai gabatar da wani muhimmin jawabi a lokacin taron, wanda za a gudanar a babban dakin taron jama'a da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China