Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.29
2020-09-07 09:35:03        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Lahadi cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar COVID-19 ya kai 31,056 a fadin nahiyar Afrika, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a nahiyar ya karu zuwa 1,291,724.

Kwararriyar hukumar lafiyar ta kungiyar tarayyar Afrika AU ta ce, adadin mutanen da suka warke daga cutar a nahiyar ya kai 1,031,453.

Nahiyar Afrika tana da kashi 5% na yawan masu dauke da cutar COVID-19 a fadin duniya.

Hukumar Africa CDC ta sanar a ranar Juma'a cewa, kasashen Afrika 9 da suka hada da Afrika ta kudu, da Habasha, da Libya, su ne ke da kashi 81% na sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Afrika a makon da ya gabata. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China