Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta baiwa bankuna da kamfanonin inshora na ketare iznin kafa hukumomin kudi kimanin 100 tun 2018
2020-09-07 10:01:16        cri

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, daga shekarar 2018 zuwa wannan lokaci, gwamnatin kasar Sin ta baiwa bankuna da kamfanoni inshora na kasashen waje iznin kafa kimanin hukumomin kudi 100 a fadin kasar. Matakin dake nuna cewa, hukumomin kudi na ketare na da tabbaci kan ci gaban tattalin arziki da harkokin kudi na kasar.

Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin bankuna da inshora na kasar Sin Zhou Liang, shi ne ya bayyana haka, yayin da yake jawabi a dandalin tattaunawar bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima ta kasa da kasa na kasar Sin (CIFTIS) da ke gudana a halin yanzu.

Zhou ya kuma bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana cika alkawuranta na kara bude kofofinta a bangaren harkokin kudi, a yayin da take ci gaba da bude kofa, da samar da manufar da ta dace ga hukumomin kudi na ketare ba tare da wata rufa-rufa ba.

Taken bikin baje kolin na bana, shi ne, "hidmimomi ga duniya, mokama ta bai daya". Bikin da ake fatan rufewa a ranar 9 ga watan Satumba, ya samu halartar baki kimanin 100,000 da kamfanoni da hukumomi 18,000 daga kasashe da yankuna 148.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China