Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kafa kwamitin bunkasa masana'antar fasahar sadarwar zamani
2020-09-07 10:17:40        cri

Kasar Sin ta kafa wani kwamitin, da zai yayata masana'antar fasahar sadarwar zamani. An dai kaddamar da kwamitin ne, a yayin bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 (CIFTIS), dake gudana yanzu haka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kwamitin zai mayar da hankali ne, a fannin dabarun bincike, da ingantaccen tsari, da kayayyakin da ake bukata da sauran muhimman sassa na masana'antar, a kokarin da ake na gina kyakkyawan tubali mai dorewa da ci gaba mai inganci a wannan fanni a kasar Sin.

Haka kuma, kwamitin zai bunkasa kirkire-kirkire a sassa da suka hada da, tsaro a wurin aiki, da samar da makamashin kwal, da kiwon lafiya, da gine-gine, da motoci da tauraron dan-Adam. Sauran sun hada, da karfafa matakan tattara bayanai, da musaya, da yadda ake zakulo muhimman bayanai a wannan bangare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China