Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" sun yi cinikayyar sama da Yuan triliyan 5
2020-09-07 10:22:18        cri
Kamfanin dillancin labarai na China News Agency ya rawaito mataimakin shugaban hukumar bunkasa cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin, Chen Jian'an, ya bayyana a birnin Xining, na lardin Qinghai cewa, a watanni bakwai na farkon wannan shekarar, kasar Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" sun yi huldar cinikayyar shigi da fici a tsakaninsu na RMB Yuan triliyan 5.03, domin tabbatar da safarar kayayyakin bukatu da kuma isassun kayayyaki karkashin yanayin da ake ciki na fama da matsalar annobar COVID-19.

Da yammacin wannan rana, an gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kula da muhallin halittu na Qinghai da kamfanonin kasashen dake hanyar "ziri daya da hanya daya" a Xining na lardin Qinghai.

Chen Jian'an ya ce, kasar Sin za ta gina wani sabon tsarin cigaba bisa ga tsarin gudanarwar tattalin arzikin kasar da kara bude kofarta ga ketare. Kyautatuwar tattalin arzikin da kasar Sin ta samu na dogon lokaci, da kara zurfafa cudanyar tattalin arziki da kasashen duniya zai samar da karin damammaki ga duniya baki daya.

A watanni bakwai na farkon wannan shekara, jarin da aka zuba na kai tsaye wanda bai shafi kudade ba tsakanin kasar Sin da kasasahen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" ya kai dala biliyan 10.27, inda ya karu da kashi 28.9 bisa 100 a makamancin lokacin shekarar bara, yayin da kasar Sin da kasashen Turai sun bude bangarori hada hada 6354, wanda ya karu da kashi 41 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar da ta gabata. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China