Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dandalin kula da lafiyar alumma na bajekolin 2020 CIFTIS ya kaddamar da shirin Beijing na yaki da annobar COVID-19
2020-09-07 11:46:14        cri

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito a ranar 6 ga wata cewa, hukumar lafiyar birnin Beijing, tare da hadin gwiwar ofishin wakilan hukumar lafiya ta duniya WHO dake kasar Sin, da sauran cibiyoyi, sun yi hadin gwiwa wajen kaddamar da shirin Beijing na dandalin kula da lafiyar al'umma a bikin baje kolin ayyukan ba da hidima na kasa da kasa da kasar Sin na shekarar 2020, inda suka bukaci a gudanar da yaki da barazanar annobar COVID-19 na bai daya a duniya.

Shirin ya bayyana cewa, ya kamata dukkan bangarori su rungumi tsarin bude kofa, da mutunta juna, da yin koyi da juna, da amfanar juna da cin moriyar juna, da samar da daidaito, da yin al'amurra a bayyane da girmama juna, kana a hada kai wajen amfani da hikimomin duniya a yaki da annobar, a jure duk wata barazanar cutuka a duniya, a kara zurfafa hadin gwiwar duk duniya a fannin kiwon lafiya, kana a kara daga matsayin tsarin kula da lafiyar alummar kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China