Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikayyar ba da hidima ta zama sabon ginshiken tabbatar da karuwar tattalin arziki
2020-09-07 13:42:13        cri

Akaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar kwanan baya sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Yulin da suka gabata, sakamakon barkewar annobar COVID-19, yawan cinikayyar ba da hidima da aka yi a kasar Sin ya ragu, amma adadin kayayyakin da suka shafi cinikayyar ba da hidima, kuma aka fitar da su zuwa ketare, ya fi irin wannan abubuwan da aka shigo da su cikin kasar Sin kyau, wato gibin cinikayyar ba da hidima ya ragu. A sabon yanayin da ake ciki yanzu, cinikayyar ba da hidima da ake yi ta zama sabon ginshike wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Rahotanni na cewa, daga shekarar 2012 zuwa yanzu, yawan kayayyakin ba da hidima da aka yi shigi da fice ya karu da kashi 7.8 cikin dari a kowace shekara a nan kasar Sin. A shekarar 2019, yawan kudin cinikayyar ba da hidima da kasar Sin ta yi shige da ficensu, ya kai fiye da kudin RMB Yuan triliyan 5.4, wannan ya alamta cewa, yanzu kasar Sin tana matsayi na biyu a duk fadin duniya wajen cinikayyar ba da hidima.

Bugu da kari, nau'o'in kayayyakin ba da hidima da kasar Sin take shige da ficensu sun kyautatu. Yanzu haka, yawan cinikayyar ba da hidima masu alaka da kwafutoci da samar da bayanai da sauran abubuwan da suke wakiltar sana'o'in ba da hidimomi da suka kunshi harkokin ilmi da fasahohin zamani, ya karu zuwa kashi 34.7 cikin dari a shekarar 2019 daga kashi 27.3 cikin dari a shekarar 2015. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China