Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta fara rabon tallafi ga mabukata ta jiragen sama a arewa maso gabashin kasar
2020-09-08 10:08:38        cri
Gwamnatin Najeriya ta shirya gudanar da rabon tallafin kayayyakin abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum ta jiragen sama ga mutanen dake cikin halin bukata a yankuna masu wahalar shiga sakamakon matsalolin ambaliyar ruwa da rashin tsaro a jahar Borno, dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Ministar ma'aikatar ayyukan jin kai ta kasar, Sadiya Umar Farouq, ta ziyarci birnin Maiduguri a karshen mako domin bayar da tallafin kayayyakin ga jahar Borno.

Ta fadawa 'yan jaridu cewa, ma'aikatarta ne za ta gudanar da aikin rabon kayayyakin tallafin tare da hadin gwiwar rundunar sojojin saman Najeriya, domin rabawa al'ummomin mazauna yankunan wadanda ba za a samu damar shiga ba, dake jahar Borno.

Ministar ta bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta tantance yankunan da ba za a samu damar shiga ba, kana za a tantance hakikanin tallafin da suke bukata.

Ta kara da cewa, za su gano wadannan wurare da kuma gano yawan mutanen dake zaune a wuraren.

Da take amsa tambaya game da yiwuwar kada mayakan Boko Haram su kwace tallafin kayayyakin abinci da za a raba ta jiragen saman, ministar ta ba da tabbacin za a gudanar da bincike ta jiragen sama domin kaucewa duk wata barazana. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China