Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saurin bunkasuwar cinikayya ta yanar gizo tsakanin Sin da sauran kasashe ya karu da kaso 56 cikin 100 a shekara
2020-09-08 10:18:48        cri

Mataimakin shugaban cibiyar hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki ta kasa da kasa ta ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, Qu Weixi, ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, saurin bunkasuwar cinikayyar yanar gizo tsakanin kasar Sin da sauran kasashe, ya karu da kaso 56 cikin 100 a shekara.

Qu Weixin ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a dandalin bikin baje kolin muhallin halittu na Qinghai da baje kolin darduna na Tibet da ya gudana a jiya. A cewarsa, tsaiko da ake fuskanta a harkokin cinikayya da kuma matsalar COVID-19, sun haifar da babban kalubale kan yadda duniya ta saba tafiyar da harkokin cinikayya a baya. Sai dai duk da haka, cinikayyar yanar gizo tsakanin Sin da sauran kasashe, tana bunkasa yadda ya kamata. A hannu guda kuma, kasar Sin tana sauyawa daga tsohon tsarin cinikayya, ta hanyar farfado da kuma daga darajar masana'antun samar da kayayyaki, da bunkasa hanyoyin jigila, da samar da kudade da hade hidimar cinikayar waje, kamar raya kamfanoni, da a halin yanzu suka kasance sabbin karfi na bunkasa cinikayyar ketare.

Alkaluma sun nuna cewa, yawan dandalolin cinkayya ta yanar gizo da ayyukan kamfanonin cinikayya ta yanar gizo a kasar Sin, suna karuwa, lamarin da ke kara haifar da yin takara. Kamfanonin da suka shahara a harkar cinikayya ta yanar gizo, galibi suna da girma da yawan hada-hada da samfura da dama, da kuma fifiko na kasuwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China