Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An zabi shugaban kasar Ghana a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS
2020-09-08 10:22:21        cri
Shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, a ranar Litinin sun zabi shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban kungiyar, gwamnatin Ghanan ta sanar da hakan.

An gudanar da zaben ne a lokacin taron kolin kungiyar ta ECOWAS karo na 57 a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer. Akufo-Addo, zai karbi ragamar shugabancin kungiyar daga shugaban Nijer Mahamadou Issoufou, inda zai shafe tsawon watanni 12 a bisa tsarin shugabancin kungiyar na karba-karba.

Shugaban kasar ta Ghana, ya jagoranci tawagar kasarsa zuwa taron na ranar Litinin, inda shugabannin na yammacin Afrika suka tattauna batutuwa dake shafar halin da ake ciki game da yaki da annobar COVID-19 a shiyyar, da kuma batun samar da kudin bai daya na kasashen ECOWAS.

A shekarar 1975 aka kafa ECOWAS, tana da mambobin kasashe 15, an kafa kungiyar ne da nufin bunkasa tattalin arziki da ci gaban shiyyar yammacin Afrika daga dukkan fannoni. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China