Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Shirin Najeriya na sauya tunanin tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba zai yi tasiri
2020-09-08 10:29:30        cri

Jami'in tsare-tsaren ayyukan jin kai na MDD dake Najeriya, Edward Kallon, ya bayyana cewa, shirin mahukuntan Najeriya game da sauyin tunanin tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba, zai taimaka wajen sake shigar da su cikin al'umma da ma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kallon wanda ya bayyana haka, yayin da ya ziyarci sansanin sauya tunanin tsoffin mayakan na Boko Haram da suka tuba dake jihar Gombe, ya ce, shirin sauya tsattsauran ra'ayi, da sake tsugunarwa da shigar da su cikin al'umma (DRR), shiri ne mai sarkakiya wajen tabbatar da zaman lafiya. Kuma tsarin ya yi tasiri a duniya.

Manufar shirin wanda na hadin gwiwa ne, tsakanin gwamnati, da sojoji da sauran ma'aikatu, da sassa da kuma hukumomi, ita ce sauya tunani da tsugunar da tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba, a kokarin da ake na yaki da ta'addanci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China