Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNEP ya kaddamar da binciken yanayin gurbacewar iska da sauyin yanayi a Afrika
2020-09-08 11:11:00        cri
Shirin kiyaye muhalli na MDD, UNEP, tare da hadin gwiwar shirin gamayyar kula da sauyin yanayi da ingancin iska CCAC a ranar Litinin sun kaddamar da kashin farko na binciken yanayin gurbacewar iska da matsalolin sauyin yanayi a nahiyar Afrika.

Juliette Biao Koudenoukpo, darakta, kuma wakiliyar ofishin UNEP ta Afrika, ta ce binciken zai taimaka wajen tattara hakikanin bayanai da ake bukata domin tantance illolin da sauyin yanayi da kuma gurbacewar iska za su haifar ga muhalli, da lafiyar bil Adama, da ma zaman rayuwar al'umma.

Koudenoukpo ta jaddada muhimmancin bayar da fifiko wajen wayar da kan al'umma, tare da bibiyar mummunan tasirin da gurbacewar iska zai haifar a Afrika, ta bayyana hakan ne a Nairobi a lokacin bikin ranar samar da iska mai inganci da sararin samaniya mai launin shude na kasa da kasa karo na farko.

Koudenoukpo ta ce, samar da iska mai inganci gami da matakan yaki da sauyin yanayi muhimman hanyoyi ne na tabbatar da kyakkyawan muhalli mai launin kore gami da ci gaban nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China